Home Labarai A na yawan kashe zabiya domin yin asiri — Ƙungiya

A na yawan kashe zabiya domin yin asiri — Ƙungiya

0
A na yawan kashe zabiya domin yin asiri — Ƙungiya

 

Jake Epelle, Shugaban Gidauniyar kula da Zabiya ya koka kan cewa a na kashe zabiya domin yin asiri yin arziki a Nijeriya da ma wasu ƙasashen Afrika.

Epelle ya yi wannan ƙorafin ne a wata tattaunawa ta musamman da Muryar Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa a Abuja a yau Lahadi.

Ya ce lokacin da a ka riƙa yaɗa cewa ƴan ƙungiyar ashirin na fito wa sun sace zabiya a ƙasashen Afirka, shi ganau ne ba jiyau ba.

Ya ƙara da cewa a 2014 ma sai da ya tsallake rijiya da baya bayan da a ka yi yunkurin sace shi.

Epelle ya ce Gidauniyar ta sa na iya kokarin ta na ta samar da kariya ga mutane masu nakasa, har da ma layikan waya na tsaro da ga ƴan sanada.

Ya yi kira ga al’umma a Nijeriya danaksashen Afirka da su dena kisan zabiya domin yin asirin kudi.