
Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa yawan mutanen duniya ya cika biliyan takwas daga jiya Talata.
Shekara goma sha ɗaya da ta gabata ne duniyar ta zarta yawan mutum miliyan dubu na ƙarshe da ta kai, amma kuma kiyasin na Majalisar ya nuna cewa duniyar ba za ta sake cimma wata miliyan dubu ɗin ba nan gaba sai a ƙarshen shekarun 2030.
Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma yi ƙiyasin cewa rabin hayayyafar da za a yi a nan gaba a duniyar baki ɗaya, ana ganin za a yi ta ne a ƙasashe takwas, biyar daga cikinsu na Afirka ne.
A shekara mai zuwa ne kuma ake sa ran Indiya za ta zarta China yawan al’umma a duniya baki ɗaya.