
Ɗan yayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Fatuhu Muhammed, ɗan majalisar wakilai a jihar Katsina, ya fice jam’iyar APC.
Muhammed shine ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Daura/Sandamu/Mai’adua a majalisar wakilai.
Ya bayyana ficewar tasa daga APC ne a wata wasiƙa, mai kwanan wata 13 ga Yuli.
A wasikar, wacce ya aike wa shugaban jam’iya na mazaɓar Sarkin Yara a Daura, Muhammed ya ce ficewar ta sa ta fara aiki nan take.
Sai dai kuma bai faɗi dalilin da ya sanya ya fice daga jam’iyar ta APC ba.
Amma kuma a watan Mayu, Muhammed ya sha kaye a zaɓen fidda-gwani na jam’iyar APC na majalisar wakilai.