Home Labarai Yin tazarar haihuwa ba ya haifar da cutar kansa

Yin tazarar haihuwa ba ya haifar da cutar kansa

0
Yin tazarar haihuwa ba ya haifar da cutar kansa

Wata kwararriyar likitar fannin haihuwa, Ijeoma Onuorah, ta ce amfani da maganin tazarar haihuwa wajen tsarin iyali baya haifar da cutar daji amma yana rage hadarin kamuwa da cutar daji.

Onuorah ta bayyana haka ne a wajen bikin Ranar Iyali ta Duniya ta 2023, wanda ma’aikatar lafiya ta jihar Anambra, tare da hadin gwiwar ma’aikatar mata da walwalar jama’a suka shirya, ranar Juma’a a Awka.

Taron wanda ake gudanarwa duk ranar 15 ga watan Mayu, an kirkire shi ne domin wayar da kan jama’a game da mahimmancin iyalai da inganta rawar da iyalai ke takawa a cikin al’umma.

Taken bikin na bana shine “Tsarin al’umma da iyalai”.

Onuorah ta bukaci iyalai da su yi amfani da duk wata hanyar kayyade iyali da suka ga dama, tana mai cewa dukkansu suna da aminci kuma suna da amfani ga lafiya da rayuwar iyali da kuma al’umma baki daya.

“Akwai jita-jita da yawa da tatsuniyoyi da ke hana iyalai rungumar tsarin kayyade iyali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mata da dama.

“Babu wata shaida da ke nuna cewa tsarin iyali yana haifar da cutar kansa, sai dai ma ya rage haɗarin kamuwa da cutar kansa.

“Amfanin tsarin iyali ya hada da dogon tazara tsakanin masu juna biyu, hana daukar ciki mara shiri da kuma inganta rayuwar jarirai saboda za a samu karin lokaci na tarbiyya da kulawa,” in ji ta.