
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz_Yari tare da ayarinsa sun sha ruwan duwatsu a Gusau, a ranar Lahadin da ta gabata, a lokacin da suke wucewa zuwa Kaduna.
Al’amarin dai, kamar yadda jaridar Daily_Trust ta ruwaito, ya faru ne a daidai shataletalen Lalan da ke garin Gusau kuma ana zargin cewa magoya bayan wasu ‘yan takarar gwamna ne suka yi jifar, domin kuwa gwamnan yana wucewa ne a daidai lokacin da dan takarar gwamna a karkashin Jam’iyyar APC kuma Mataimakin Gwamna a yanzu, Malam Ibrahim_Wakkala ke gudanar da taro.
Bayanai sun nuna cewa, ‘yan takarar suna adawa ne da matakin da gwamnan ya dauka, na nuna goyon bayansa ga Kwamishinan Al’amuran Kudi, Mukhtar_Shehu_Idris a zaben 2019 mai zuwa.
Da yake maida martani dangane da wannan ruwan duwatsu da ya sha a Gusau, Gwamna Yari, ta bakin jami’i mai ba shi shawara ta bangaren Watsa Labarai, Ibrahim_Dosara, ya yi Allah-wadai da al’amarin sannan ya yi kira ga magoya bayan APC da su guji tayar da fitina ko shirya tarukan da ba su halalta ba a doka.