
Shugaban Kamfanin Mai, NNPC, Mele Kyari ya ce farashin man fetur zai iya kaiwa naira N320 zuwa N340 kowacce lita daga shekara mai zuwa ta 2022.
Ƙasa da mako guda kenan da hukumar Bada Lamuni ta Duniya, IMF ta baiwa gwamnatin Nijeriya shawarar cire tallafin man fetur domin karkata kuɗaɗen da take zubawa zuwa ayyukan raya kasa
Yayin da ya ke gabatar da jawabi a wani taro na bankin duniya yau Talata a Abuja, Kyari yace tabbas babu abinda zai hana cire tallafin man a shekara mai zuwa, domin kuwa dokar da ake amfani da ita wajen biyan tallafin zata daina aiki daga ƙarshen watan Fabarairu mai zuwa.
Shugaban kamfanin man yace a shekara mai zuwa babu wani tanadi da akayi na sanya kudin tallafin, kuma ganin yadda ayyuka suka yi wa gwamnati yawa, zasu aiwatar da shirin janye shi a cikin sauki.
Dangane da tashin farashin iskar gas da ake girki da shi kuwa, Kyari yace batu ne na ƙaruwar buƙatar sa ta haifar da hauhawan farashin tare da karancin sa a kasuwannin duniya.
Shugaban kamfanin NNPC yace dama iskar gas bashi da wani tallafin da gwamnati take sanyawa, saboda haka farashin sa na tafiya ne da yadda kasuwar duniya take a koda yaushe.
RFI ta rawaito Kyari ya bayyana cewar kamfanin NNPC na iya bakin kokarin sa wajen kara yawan iskar gas din da ake sayarwa a cikin gida domin biyan bukatar masu aiki da shi.
Ita kuwa ministar kudi, Zainab Ahmed cewa tayi gwamnati zata cire tallafin domin baiwa ‘Yan Najeriya matalauta naira N5,000 kowanne wata a matsayin tallafin sufuri.
Ministar tace akalla ‘Yan Najeriya miliyan 30 zuwa 40 ake saran su ci gajiyar shirin.