Home Labarai Da yiwuwar mu janye yajin ai nan da kwanaki kaɗan — ASUU

Da yiwuwar mu janye yajin ai nan da kwanaki kaɗan — ASUU

0
Da yiwuwar mu janye yajin ai nan da kwanaki kaɗan — ASUU
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, Emmanuel Osodeke, ya bayyana fatansa na ganin cewa yajin aikin na tsawon watanni 7 da kungiyar ta ke yi zai kawo karshe nan da ƴan kwanaki.
Ya bayyana hakan ne a jiya Litinin  yayin wata ganawa da shugabannin majalisar wakilai, karkashin jagorancin kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila.
A yayin da ya ke yaba wa shugabannin majalisar kan sa baki domin kawo karshen yajin aikin da aka dade ana yi, Osodeke ya yi fatan cewa yajin aikin da za su iya biyo baya ba za su dade ba.
“Don Allah, mu hada kai domin kawo karshen wannan abin da muka faro, domin kowane dan Nijeriya ya yi alfahari da cewa muna da jami’o’i da za mu yi alfahari da su.
“Har ila yau, ina so in gode muku. Ina kuma mika godiyarmu ga shugaban kasa da ya sa baki, ina so in yi kira a nan gaba kada mu bar yajin aikin ya daɗe. Bai kamata yajin aikin ya wuce kwanaki biyu ba,” in ji shugaban ASUU.
Osodeke ya kuma caccaki Ministan Ilimi Adamu Adamu da takwaransa na Kwadago da Aikin yi, Chris Ngige bisa rashin da cewa da su ka nuna wajen tafiyar da rikicin yajin aikin.