
Tsohon Gwamnan jihar Yobe Alh. Bukar Abba Ibrahim ya hakura da neman kujerar Sanata ta yankin Zone A a jihar Yobe. Sannan kuma ya mara baya ya Gwamna Geidam ya tsaya takara domin neman Sanata.
Bugu da kari Sanata Bukar Abba ya goyi bayan Mai Mala Buni a matsayin dan takarar Gwamnan jihar da Geidam ya tsayar.
Wannan ya faru ne a sakamakon wani Zaman sulhu da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.