
Hukumar binciken sararin samaniya ta Najeriya NiMet ta bayar da bayanin cewar a gobe talata za a wayi gari da hazo mai yawa a mafiya yawancin jihohin Arewancin Najeriya.
A wata sanarwa da hukumar ta ftar a ranar litinin, hukumar tace, Hazon zai yi sauki a mafiya yawancin jihohin Kudancin Najeriya, yayinda a Arewa abin zai yi kamari, sai dai, sanarwar tace ana sa ran gari zai fara washewa a ranar Alhamis.
A dan haka ne masana kiwon lafiya suke bayar da shawarar mutane su yi amfani da abinda ka iya rufe musu hanci domin gudun shakar skar da ka iya yi musu illa.