Home Labarai Za mu fara yankewa fulani makiyayan irin hukuncin da muke yi wa ‘yan fashi a Delta

Za mu fara yankewa fulani makiyayan irin hukuncin da muke yi wa ‘yan fashi a Delta

0
Za mu fara yankewa fulani makiyayan irin hukuncin da muke yi wa ‘yan fashi a Delta

Daga Hassan Y.A. Malik

Kwamishinan ‘yan sandan jahar Delta, Muhammad Mustafa ya ce daga yanzu za su dauki Fulani Makiyaya masu daukan mukamai kamar yadda su ke daukan ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

Mustafa ya fadi haka ne a yayin da ya ke magana da manema labarai a Asaba, babban birnin jihar.

Ya ce tuni rundunar ‘yan sandan jahar ta fara aiki tukuru wajen ganin ta kwace makaman da ke hannun wasu daga cikin Fulani makiyayan.

A cewar shi “Akwai Fulani makiyaya na gaskiya, wadanda ke bin doka, amma duk makiyayin da muka gani da makami za mu dauke shi ne kamar dan fashi ko mai satar mutane”.

Kwamishinan ya ce sun bada kwanaki 21 daga 1 ga watan Maris, domin mutane su mika makaman su ga rundunar ‘yan sandan jahar, domin kuwa da zaran wannan wa’adi ya cika za su shiga kama masu daukan makamai su kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya ce wadanda abun ya shafa sun hada da fulani makiyaya, ‘yan bijilanti, maharba, masu gadi da sauransu.