
Shugaban kasa Tinubu ya taya murna ga dan takarar jam’iyyar APC, a zaben Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo bisa nasarar lashe zaben da ya yi.
A juya Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta sanar da Sanata Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
A sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan fannin yada labarai da dabarun mulki , Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yabawa shugabannin APC na kasa da na jihar Edo da Gwamnonin jam’iyyar bisa aiki tukuru wajen nasarar ta a zaɓen.
Shugaban ya ce, nasarar ta nuna goyan bayan da al’umma ke bai wa manufofin gyaran tattalin arziki, da ma salon mulkin da APC.
Shugaban ya kuma yi kira ga wadanda su ka samu rashin nasara da su yi amfani da hanyoyin shari’a wajen mika kokensu.
Shugaban ya kuma godewa INEC da jami’an tsaro bisa tabbatar da an yi zaben cikin nasara.
“Ina yabawa hukumar zabe ta INEC da hukumomin tsaro bisa aiki ba dare ba rana wajen gudanar da zaben cikin lumana”