
Daga Ado Abdullahi
Jihar Osun ɗaya ce daga cikin jihohin da jam’iyyar APC ke taƙama da ita. Domin tana cikin tsakiyar jihohin Yarabawa da jam’iyyar ta APC take da mulki. Jihohin sune jihar Kwara, Ekiti, Ogun, Oyo da Ondo. Jihar dai tana da muhimmanci a siyasance a jihar domin nan ne Jihar Shugaban jam’iyyar APC na farko wato Cif Bisi Akande. Akanden dai shi ne tsohon gwamnan Jihar a 1999-2003 a tsohuwar jam’iyyar Yarabawa ta AD. Kuma har yanzu sune masu faɗa a ji a jam’iyyar ta APC.
Sakamakon zaɓen ranar Asabar 22 ga watan Augusta ya zo da mamaki ga jam’iyyar ta APC. Domin kayen da ɗan takarar gwamna mai ci wato Malam Rauf Aregbesola ya sha a hannun ɗan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP wato Ademola Adeleke, ya bai wa maraɗa kunya. Ɗan takarar na jam’iyyar PDP ya sami ƙuri’a 254,698 inda abokin hamayyarsa ta APC ya sami ƙuri’u 254,345. Jam’iyar SDP kuma ta sami ƙuri’u 128,049 a zaɓen.
Tabbas gwamnatin Malam Rauf Aregbesola ta wahalar da al’ummar jihar ta Osun wajen daƙile musu kuɗaɗensu na albashi da rashin kawo cigaba ga al’ummar jihar. Haka nan mutanen Osun sun ƙalubalanci gwamnatin Buhari wacce ta ƙaƙabawa mutanen ƙasar nan talauci, fatara da yunwa. Haƙiƙa al’ummar Osun suna da dalilin fatali da ɗan takarar jam’iyar ta APC.
Irin wannan zaɓen ya faru a zaɓen Sanata ta kudancin jihar Bauchi inda jam’iyyar ta APC ta sha da ƙyar a hannun jam’iyyar ta PDP da sauran ƴan hamayya.
Jihar Bauchi tana ɗaya daga cikin jihohin da zamu iya cewa jihar ƴan a mutun Baba Buhari ce. Wato tun farkon takarar Shugaba Muhammadu Buhari yake samun rinjaye a duk zaɓen da ya shiga daga jihar. Ba ma shi ba duk wanda ya ɗaga hannunsa ya kan ci albarkacin Baba Buhari da ƙuri’u masu tazara da yawa. Toh amma sai ga shi APC sun sha da gumin goshi a hannun ƴan adawa.
A jihar ne aka ƙirƙiro taken a kasa a tsare a raka. Duk dai don bayar da kariya ga kuri’un da aka kaɗa. A jihar ne matasa kan kwana a sakatariyar hukumar zaɓe ta ƙasa wato INEC, wai duk domin kare abin da suka zaɓa gudun kada a yi musu aringizon ƙuri’u. Toh amma sai gashi sun kunyata jam’iyyar ta APC.
Waɗannan zaɓuɓɓuka wata ƴar manuniya ce ga zaɓen 2019, inda alamu suke nuna jam’iyyar APC za ta kwashi kashinta a hannu a mafi yawan jihohin da take mulki a halin yanzu. Da kuma uwa uba zaɓen shugaban ƙasar mai zuwa inda ƴan Nijeriya suka shirya tsaf wajen korar wannan gwamnatin mai ɗimbin alƙawarra babu cikawa.
Tabbas matuƙar jam’iyyar PDP ta ƙasa ta yi zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa cikin adalci. Kuma sauran ƴan takara suka dafawa duk wanda aka zaɓa, toh kayar da gwamnatin APC wani abu ne da zai zo cikin sauƙi. Hakanan a matakan jihohi, dukkanin alamu da lissafi irin na siyasa ya nuna duk inda ƴan adawa suka sami haɗin kai toh zasu iya hamɓarar da gwamnatocin APC a matakan jiharsu. Domin duk jihohin talakawa sun gaji da mulkin kama karya da ake yi musu.
Babban abin farin ciki shi ne yadda manyan ƴan takarar neman shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP suke ta nanatawa cewar duk wanda Allah Ya bai wa damar samun tikitin zaɓen fidda gwani a cikinsu, toh sun yi alƙawarin bashi goyon baya domin a cimma nasara.