Home Labarai Zainab, wacce ta tsallake hukuncin kisa a Saudiya bayan an mata sharrin safarar ƙwaya, ta zama jami’ar NDLEA

Zainab, wacce ta tsallake hukuncin kisa a Saudiya bayan an mata sharrin safarar ƙwaya, ta zama jami’ar NDLEA

0
Zainab, wacce ta tsallake hukuncin kisa a Saudiya bayan an mata sharrin safarar ƙwaya, ta zama jami’ar NDLEA

 

Zainab Habibu, matashiyar da Saudiya Arebiya ta kama da zargin safarar miyagun ƙwayoyi, ta zama jami’ar yaƙi da miyagun ƙwayoyi, Nacortic Officer ta Hukumar yaƙi da sha da Dataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA.

Zainab, wacce ta kammala karatunta a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Jihar Kano, ta gamu da ibtila’in ne a shekarar 2018 a yayin tafiya zuwa Ummara ita da mahaifiyar ta inda wasu ɓata-gari su ka yi mata canjen jaka su ka bata mai ɗauke da ƙwaya.

Amma, bayan da a ka tsananta bincike, sakamakon sa bakin mahukunta daga Nijeriya, sai a ka gano cewa Zainab ba ta da laifi inda Saudiya ta sake ta ta dawo gida Nijeriya.

Tun bayar dawowarta ba a sake jin ɗuriyar Zainab ba sai kawai ganin hotunanta a ka yi a yanar gizo da kayan NDLEA inda ta gama ɗaukar horo.

A halin yanzu dai Zainab ta zama cikakkiyar jami’a mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi inda a ke ta yi mata fatan alheri a kafafen sadarwa.