
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bayyana cewar za’a rabawa ‘yan Najeriya dala miliyan 320 kudaden da Abacha ya sata ya boye a kasashen waje lokacin da yake Shugaban kasa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a taron karawa una sani na kasashen rainon Ingila reshen Afurka akan yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arziki ta’annati dake gudana a ABuja babban birnin Najeriya.
SHugaban wanda mataimakinsa Yemi Osibanjo ya wakilta, Buhari ya bayyana cewarwannan shi ne sharadin da kasar Suwizalan ta bayar yayin da take danka kudin ga Najeriya.