Home Kanun Labarai Zamu samar da cibiyar tunawa da Shehu Shagari – Buhari

Zamu samar da cibiyar tunawa da Shehu Shagari – Buhari

0
Zamu samar da cibiyar tunawa da Shehu Shagari – Buhari

Yayin da ya isa jihar Sakkwato domin yiwa Gwamnati da iyalan Tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari ta’aziyar rasuwarsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhinin sa na rasuwar Shagari. Ya Kara da cewar dole ne Gwamnati ta samar da cibiyar tunawa da tsohon Shugaban kasar akan irin gudunmawar dabya bayar don ciyar da Najeriya gaba.

Shugaban kuma yayi bayanin cewar babu wata tsattsamar dangantaka tsakaninsa da marigayi Shehu Shagari kamar yadda wasu ke tunani.