
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar litinin ya sha alwashin ganin an sako dukkan mutanan da Boko Haram suka sace, ciki kuwa har da ‘yan matan Dapchi guda 110 da aka sace a makon jiya a makarantar sakandiren Gwamnati dake jihar Yobe.
Shugaban kasa yayi wannan albishir ne a fadar Gwamnati dake Villa, Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin Malaman jami’ar Maiduguri guda uku da aka sace, da kuma wasu mata da aka kubuto da su daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram da suka sace su.
A wasu bayanai da ya dinga fitarwa ta shafinsa na Twitter @MBuhari, Shugaban kasa ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewar babu wani mutum da gwamnati zata bari a mula a hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.
“Ba zan iya gaya muku irin farincikin da nake ciki ba a yau, ace dai gashi mun karbi ‘yan uwan daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram da suka sace su, iyaye. da ‘ya ‘ya. Zamu yi dukkan mai yuwuwa wajen ganin bamu bar wani ya saraya a hannun ‘yan ta’adda ba”
Shugaban ya kara da cewar “Su din Malamai ne na jami’ar Maiduguri, an sace su a lokacin da suke yiwa kasarsu aiki, haka kuma, an sace wasu mata da suka je ta’aziya”
“Yau cikin murna da farin cikin dawowarsu lafiya muke yi cikin dangi da iyalansu”
“Sun bayyana min cewar har sun fitar da ran cewar zasu fito daga hannun wadan da suka sace su da ransu. Na tabbatar musu cewar ba zamu taba barin rayuwar wani ta saraya ba”
“Na baiwa dukkan jami’an tsaro umarni da su tabbatar da cewar dukkan wadan da aka sace an dawo da su, ciki kuwa har da ‘yan matan Dapchi”