Home Siyasa Zan canja halayyar saɓa lokaci idan na zama gwamna a Kano — Ɗan takarar PRP

Zan canja halayyar saɓa lokaci idan na zama gwamna a Kano — Ɗan takarar PRP

0
Zan canja halayyar saɓa lokaci idan na zama gwamna a Kano — Ɗan takarar PRP

 

 

 

 

 

Ɗan takarar gwamna na jam’iyar PRP a Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana rashin jin daɗinsa da halayyar nan ta saɓa lokaci.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa saɓa lokaci ya zama al’adar ƴan nijeriya da ma nahiyar Afrika, inda a turance a kai masa laƙabi da “African Time”.

 

Yakasai ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “ƴan Nijeriya da ‘African time’, wannan na ɗaya da ga abubuwan da zan kawo canji a kai idan na zama gwamna, in Sha Allah.

“Idan an saka lokacin yin taro ƙarfe 10 na safe, to gwamna zai kasance a wajen tun ƙarfe 9:55 na safe,” in ji Yakasai.