
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Mista Peter Obi, ya bayyana tsarin tallafin man fetur da ake yi a halin yanzu a matsayin zamba, yana mai cewa zai bayar da wani zaɓi, idan aka zabe shi a matsayin shugaban ƙasa.
BBC Hausa ta rawaito cewa da ya ke magana jiya a wata hira kai tsaye a gidan Talabijin na Arise, dan takarar shugaban kasar ya ce tallafin man fetur ba shi da alfanu ga tattalin arzikin kasar, inda ya yi alkawarin ba zai barnatar da dala biliyan 40 a matsayin tallafi kamar yadda a halin yanzu gwamnatin APC k yi ba.
Biyan tallafin man fetur ya lakume Naira Tiriliyan 1.27 a cikin watanni biyar da suka wuce, kusan kashi 31 cikin 100 na Naira Tiriliyan 4 da aka tanada a shekarar.
Hakan ya janyo rugujewar ribar man fetur yayin da Kamfanin Mai na Najeriya, NNPC, ya kasa tura kudaden shiga zuwa asusun tarayya.
“Mun kashe sama da dala biliyan 40 wajen bayar da tallafi. Adadin kudin da muka kashe a fannin ilimi a cikin shekaru 10 da suka gabata ya kai kimanin Naira tiriliyan 8 kimanin dala biliyan 20’’ in ji shi.