Home Labarai Zan duba yiwuwar buƙatar ku ta sakin Kanu, Buhari ya faɗawa inyamurai

Zan duba yiwuwar buƙatar ku ta sakin Kanu, Buhari ya faɗawa inyamurai

0
Zan duba yiwuwar buƙatar ku ta sakin Kanu, Buhari ya faɗawa inyamurai

 

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya baiyana cewa zai duba yiwuwar buƙatar inyamurai ta sakin Shugaban Ƙungiyar Ƴan Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu ba tare da hukunci ba.

Buhari ya faɗi hakan ne lokacin ya karɓi baƙuncin jagororin inyamurai ɗin, ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan sufurin sama, Mbazulike Amaechi a fadar shugaban ƙasa a ranar Alhamis.

A sanarwar da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adeshina ya fitar, Buhari ya baiyana cewa wannan buƙata ta su mai wuya ce, musamman ma da batun na Kanu na gaban kotu.

Buhari ya kuma yi wa baƙin nasa bayani cewa tun da an riga an gurfanar da Kanu, to idan ya yi katsalandan a maganar, to ya zama ya shure tsarin cin gashin kai tsakanin ɓangaren mulki da ɓangaren shari’a kenan.

“Gaskiya kun kawo mini buƙata mai matuƙar wahala a matsayi na na shugaban ƙasa. Gaskiya akwai haɗari babba ga wannan buƙata ta ku.

“Tun hawan mulki na shekaru 6 da su ka wuce, ba wanda zai ce na yi katsalandan a harkar sharia.

“Allah Ya maka nisan kwana, ya kuma yi maka baiwar riƙe abubuwa a ƙwaƙwalwar ka. Yawancin mutane ma su rabin shekarun ka ma a ruɗe su ke. Amma wannan buƙatar ta ka akwai nauyi, amma dai zan duba,” in ji Buhari

A nashi ɓangaren, Amaechi ya nuna baƙin ciki a bisa yanayin tsaro a kudu-maso-gabas, in da ya ce tattalin arzikin yankin ya girgiza.