Home Siyasa Zan fita daga jam’iyyar PDP kafin ƙarshen watan Maris — Kwankwaso

Zan fita daga jam’iyyar PDP kafin ƙarshen watan Maris — Kwankwaso

0
Zan fita daga jam’iyyar PDP kafin ƙarshen watan Maris — Kwankwaso
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP mai hamayya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai fice daga jam’iyyar kafin karshen wannan watan na Maris.
Tsohon gwamnan ne ya tabbatar wa BBC Hausa wannan labari, inda ya ce ya yi nisa a shirinsa na komawa jam’iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.
Wani makusancin tsohon gwamnan ya ce babu tsari a game da yadda ake tafiyar da sha’anin jam’iyyar ta PDP, lamarin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara kayansa domin ya fice daga cikinta.
A watan jiya ne Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.
A baya dai, Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda jam’iyyar PDP take kokarin mayar da shi dan bora duk da gudunmawar da yake bayarwa a cikin jam’iyyar.
An daɗe ana kai ruwa rana tsakanin tsohon gwamnan na Kano da ɓangaren tsohon m5inistan Harkokin Waje, Aminu Wali.
BBC ta rawaito cewa Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP ne daga jam’iyyar APC bayan zaɓen 2015, sakamakon takun-saƙar da aka riƙa yi tsakaninsa da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A shekarar 2019, ya tsayar da tsohon Kwamishina a gwamnatinsa, Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar ta Kano, ko da yake ya sha kaye a hannun Gwamna Ganduje.