
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya ce a shirye ya ke da ya rantse da Al-ƙur’ani kan cewa bai yi sata ba a lokacin da ya ke mulkin jihar.
Daily Trust ta rawaito cewa El-Rufai ya ce ya shiga siyasa ne don ya hidimtawa al’umma ba wai don neman kudi ko satar dukiyar jama’a ba.
Trust ta ce ya yi bayanin hakan ne a yayin wani shirin Hausa na Gidan Rediyon Freedom a jihar Kaduna a yau Talata.
El-Rufai ya yi bayanin cewa ya wadatu da abinda ya ke da shi tun kafin ya zama Gwamna.
A tuna cewa majalisar dokokin jihar Kaduna dai ta yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira Biliyan 423 a lokacin mulkinsa na shekaru 8.
Tsohon Gwamnan da hadiman sa sun musanta zargin na majalisar.
Ya ce, “Na yi shiru ne kawai don ganin yadda abubuwa za su kasance, amma ni a ko da yaushe ina rokon Allah ya taimake ni a duk abinda nake a rayuwata, a matsayina na dan Adam, a koyaushe ina kokarin kaucewa yin ba daidai ba ko cin amanar al’umma.”
Sannan tsohon Gwamnan ya ce ana gayyatar mutanen sa zuwa ICPC da EFCC don kawai a bata musu suna, a don haka ya bar lamarin ga Ubangiji.