Home Labarai Ba zan kai ɗa na makarantar boko ba sai ta allo, magidanci ga shaida wa kotu

Ba zan kai ɗa na makarantar boko ba sai ta allo, magidanci ga shaida wa kotu

0
Ba zan kai ɗa na makarantar boko ba sai ta allo, magidanci ga shaida wa kotu

 

 

 

 

 

A yau Alhamis ne dai wani magidanci mai shekaru 47, Isah Magaji ya shaidawa wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rigasa, Kaduna cewa yana son ɗansa ya zama almajiri idan ya cika shekaru bakwai.

Magaji wanda ke zaune a unguwar Rafin Guza ya bayyana cewa shi ma ya yi almajirci ne lokacin yana ƙarami.

“Ni buri na shi ne na tura yaro na makarantar almajiranci a Zariya.

“Ba na son ya shiga makarantar firamare ko sakandare ta boko sabo da iyaye na ma makarantar allo su ka tura,” in ji shi.

Ya miƙa wannan bukata ne bayan da alƙalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya bada umarnin a bar yaron a hannun mahaifiyarsa Ruqayya Lawal kuma toshuwar matar Magaji.

Sai dai kuma Alkalin ya yanke hukuncin cewa Ruqayya Lawal ta riƙe yaron ɗan shekara biyu.

Ya kuma umarci Magaji ya riƙa biyan N6,000 duk wata a matsayin kuɗin ciyar da yaron.

Alkalin kotun ya kuma umarci uwar da ta mika yaron ga mahaifinsa da zarar ya cika shekaru bakwai.

Abubakar-Tureta ya kuma umurci Magaji da ya kula da kayan sawa, makaranta da kuma lafiyar yaron.

Dangane da batun kai yaron makarantar almajiri, alkalin ya ce bai dace a sake maimaita kuskuren da iyayensa suka yi a baya ba.

Ya bukaci wanda ake kara ya kai yaronsa makarantar boko da kuma makarantar islamiyya da ke kusa.