
Ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a ƙasa idan ya ci zaɓen 2023.
Kwankwaso, tsohon ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai ɓullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da ƙasa gaba, kamar yadda jaridar Leadersip ta ruwaito.
Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.
Ya bayyana cewa zamansa a fadar shugaban kasa, rashin tsaro da ya addabi al’ummar kasar a ‘yan kwanakin nan, zai zama tarihi.
Ya ba da tabbacin samar da ingantaccen ilimi da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su taimaka wajen raya arzikin kasa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya na gida da na kasashen waje da su hada kai wajen zaben sa a matsayin shugaban kasa.
“Zan magance matsalar rashin tsaro, na samar da ilimi mai inganci da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su iya daga al’ummar kasar zuwa kan tudun mun tsira.”
A jawabinsa tun da fari, shugaban NNPP na jihar Kuros Riba, Tony Odey, ya bayyana cewa zaman Kwankwaso a kan kujerar shugaban kasa, matsalar rashin tsaro za ta zama tarihi.
cewarsa: “Najeriya za ta samu idan aka zabi Kwankwaso. Duk da cewa an mayar da Siyasar Najeriya ta zama wasa da daloli, mun samu wani fitaccen mai gina kasa, wato Engr. Rabiu Kwankwso.
“Kwankwso ya zo da kwarin gwiwar da muka cancanta. “Najeriya na muradin ganin sauyi kuma mutum daya tilo da zai iya haifar da wannan sauyi shine Kwankwaso.”
“Ya yi yaki da rashin tsaro a lokacin da yake mulki a matsayin gwamnan jihar Kano ba tare da zubar da jini ba. Ina ganin idan muka ba shi dama zai iya yin irin haka a shugabancin Najeriya.”