
Hukumar kula da Aikin Gwamnati ta Ƙasa, FCSC, ta ci alwashin hana amfani da kudi wajen ɗaukar aiki da karin girma ga ma’aikatan gwamnati a kasar nan.
Farfesa Tunji Olaopa, Shugaban FCSC ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan rantsar da su da shugaba Bola Tinubu ya yi a fadar shugaban kasa a yau Laraba a Abuja.
Ya ce mambobi 12 na hukumar za su tabbatar da cewa ajandar sabuwar Nigeriya ta shugaban kasa zai zama jagora wajen gudanar da ayyukansu ga ma’aikatan Najeriya.
Olaopa ya ce hukumar za ta farfaɗo da martabar aikin gwamnati don zama wani ma’auni na ƙima da aiki yadda ya dace.
”Zarge-zargen cin hanci da rashawa na da matukar tayar da hankali. Hukumar, bisa ga tunaninta, ya kamata ta zama fitilar gaskiya kuma wadanda suka kafa hukumar a zamanin ma’aikata masu daraja sun samar wa aikin gwamnati ƙima.
‘’Saboda haka, na damu da cinikin ɗaukar aiki da ake yi a aikin gwamnati, kuma za mu yi duk mai yiwuwa tare da hadin gwiwar wasu jami’an leken asiri da tsaro don magance matsalar.
”Za mu sanar da sabbin tsare-tsaren mu a hukumar ma’aikata. Wannan shi ne zai zama cajin mu na farko kuma dukkanmu za mu himmatu wajen dawo da martabar hukumomi ga aikin gwamnati a Najeriya,” inji shi.