
Ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashi takobin mika wa gwamnatocin jihohin kasar dukkan jami’o’in da ke karkashin kulawar gwamantin tarayyar kasar idan aka zabe shi a amatsayin shugaban kasar a shekara mai zuwa.
Atiku na jawabi ne yayin wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a babban birnin kasuwanci na kasar wato Legas.
Jaridar daily Trust ta ruwaito Atikun na cewa kadarorin da Najeriya ta mallaka na iya karewa nan ba da dadewa ba:
“Daya daga cikin abubuwan da na shirya yi shi ne karfafa wa bangaren ‘yan kasuwa – na cikin gida da na waje – da su zuba jari a banagren ilimi domin Najeriya ba ta da kadarorin da za su dade tana sarrafa su kamar yadda take yi a yanzu.”
Ya kuma yi tsokaci kan talaucin da ya addabi yawancin ‘yan kasar, yana cewa “tun bayan da Najeriya ta koma bisa turbar dimokradiyya a 1998/99, kasar ba ta taba samun kanta cikin tasko kamar wanda ta ke ciki ba a yanzu.”
.