
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADP a Jihar Kano, Mallam Sha’aban Sharada, ya tabbatar wa da Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa, NMA, reshen Jihar Kano cewa idan ya ci zaɓe a 2023, zai maida Kano cibiyar zuwa ziyarar neman lafiya a ɗaukacin nahiyar Afirka.
Sharada, wanda shine ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar Kano Municipal a majalisar tarayya, ya bada wannan tabbaci ne a wata wasiƙa da ya aike wa NMA a yayin muhawarar da ta shirya wa ƴan takarar gwamna na jihar, kan ƙudirorinsu na inganta harkar kiwon lafiya idan sun ci zaɓe, wanda ya gudana a jiya Alhamis a Kano.
A wata sanarwa da Abbas Yushau Yusuf, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Sharada ya fitar a yau Juma’a, ɗan takarar ya yi takaicin rashin halartar muhawarar, inda ya ce ya na can ƙasar Saudiyya ne ya na tattauna wa da masu ruwa da tsaki a kan tanadin ayyukan ci gaba da ya ke yi wa jihar Kano, ciki har da batun lafiya.
A wasiƙar, a cewar kakakin, Sharada ya ci alwashin maida Kano ya zama gurin da baƙi za su rika zuwa da ga kasashe daban-daban na Afirka domin neman lafiya.
Dan takarar ya ce zai haɗa gwiwa da NMA da sauran masu ruwa da tsaki a harkar lafiya don ganin an inganta ta a jihar.
Ya ci akwashin tabbatar da kasafin kudin mai gwaɓi a harkar lafiya da kuma tabbatar da an yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace.
Ya kuma tabbatar wa da NMA cewa zai kula da walwala e ma’aikatan lafiya a jihar idan har ya ci zaɓe a 2023, inda ya yi alkawarin bunƙasa asibitorcin sha-ka-tafi a ƙananan hukumomi 44 na jihar domin sauƙaƙa wa al’umma wajen samun ingantaccen kiwon lafiya.
Ya kuma nuna rashin jin daɗi bisa rashin samun damar halartar taron muhawarar, inda kuma ya ce Mataimakin takararsa, Rabi’u Bako ne ya wakilce shi a wajen.