
Dan takarar shugabancin kasa ma jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi alkawarin mayar da ƴan damfarar yanar gizo, wadanda aka fi sani da “Yahoo boys,” zuwa kwararru kan fasahar zamani idan a ka zaɓe shi a babban zaben bana.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin gangamin yakin neman zabensa a jiya Alhamis a Benin, babban birnin jihar Edo.
A cewarsa, za a samar da cibiyoyin masana’antu da fasaha domin sanya matasa su zama wani sinadari na ci gaba.
Ya ce: “Zan canza yaran Yahoo kuma in sa su zama masu amfani ta hanyar canza hazaka da basirarsu don kere-keren na’urori ga masana’antu.
“Za mu iya kayar da talauci, jahilci da rashin matsuguni. Muna da ilimi, muna da kwakwalwar da za mu yi. Ku amince da ni.
“Ni kwararre ne wajen gano hanya inda babu hanya. Na sami hanyar da na bi na mayar da Atlantika akbar amfani a Legas, inda na mayar da shi wajen neman kudi.
“A ilimin da mu ke da shi, za mu iya yin tsaunuka, za mu iya hawan dutsen Kilimanjaro, za mu iya kayar da talauci. Za mu karya kangin talauci da jahilci da rashin matsuguni”