Home Siyasa Zan mara wa Tinubu baya don shi ya fi dace wa ya mulki Nijeriya — Buhari

Zan mara wa Tinubu baya don shi ya fi dace wa ya mulki Nijeriya — Buhari

0
Zan mara wa Tinubu baya don shi ya fi dace wa ya mulki Nijeriya — Buhari

 

 

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari  ya ce, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne mutumin da ya fi dacewa ya gajeshi a takarar shugabanci a Najeriya.

Tinubu ya samu tikitin takara a APC a zaɓen fitar da gwani da aka kammala jiya Laraba a Abuja.

Shugaban a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Malam Garba Shehu, na cewa yana tare da Tinubu kuma zai mara ma sa baya wajen cimma nasara a zaɓen 2023.

Ya kuma ce Tinubu shi ne mutumin da zai kare da inganta tsarin dimukuradiya da suka gina kasar a kai.

Shugaban ya kuma bukaci ‘ya’yan jam’iyyar su hada kai wajen cimma nasara a zaɓen 2023.