
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin mayar da jiharsa ta kogi tamkar kasar Holan ta fannin samar da kindirmo da nama da sauran kayan bukatun yau da kullum.
Mista Bello ya sha wannan alwashin ne, a wani taron karawa juna sani da aka gudanar kan harkar noma, a ranar Juma’a a birnin Lakwaja a jihar Kogi; taken taron shi ne, “Ciyar da harkar noma zuwa ga”
“A kasar holan, kowa ya san cewar, kasar na samar da madara da kindirmo da nama wanda galibi ake amfani da shi a kasashen Turai”
“A sabida haka,nima zan mayar da jihar Kogi a zama Holan din Najeriya, mutane zasu dinga zuwa Kogi suna sayen Nama da Kindirmo da madara”
“Mutane zasu sha mamakin yadda za’a dinga zuwa jihar Kogi sayan Nama da kindirmo da kirgi da kashi da kaho, kai har da kashin shanu sai an zo wajenmu an saya”
“Muna neman hanyar da zamu tallafawa al’umma su samu abin yi ba tare da dogaro ga aikin Gwamnati ba”
“Idan har ka mallaki fili kuma baka amfani da shi, to kana zaune masu neman haya zasu zo neman hayarsa a wajen ka”
“Zamu ilimantar da matasanmu da mata yadda zasu koyi kiwon shanu da zai basu riba mai gwabi” A cewar Gwamnan jihar Kogi.
Ma’aikatar Ayyukan gona ta kasa da kuma kungiyar IITA ne suka shirya wannan taron karawa juna sani kan shanin noma da ayyukan cigaba.
NAN