
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya yi alkawarin kara yawan jami’an tsaron Najeriya da kashi 400 idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Kwankwaso, wanda ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jihar Jigawa a jiya Lahadi, ya bayyana cewa adadin jami’an tsaro a halin yanzu yayi kaɗan.
Kwankwaso ya ce “adadin ‘yan sandan Najeriya, sojoji, jami’an tsaron farin kaya da jami’an tsaron na civil defense da duk wasu jami’ai dake damara ba su da yawan da zasu magance matsalolin tsaro da kasar nan take fuskanta”.
A cewarsa “idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Najeriya kuma idan aka kwatanta da yawan jami’an tsaro, babu yadda za a yi su magance aikata laifuka a Nijeriya”.
“In Allah ya yarda idan na zama shugaban ƙasa, zan ninka adadin ƴan sanda, Sojoji, jami’an tsaron farin kaya DSS da dai sauransu da kashi 400 cikin 100”, in ji Kwankwaso.