Home Nishaɗi A 2022 zan raba kyautar sama da N250m da na bayar a 2021 — Davido

A 2022 zan raba kyautar sama da N250m da na bayar a 2021 — Davido

0
A 2022 zan raba kyautar sama da N250m da na bayar a 2021 — Davido

 

Mawakin zamani nan a Nijeriya, David Adeleke, wanda a ka fi sani da Davido ya bayyana cewa zai raba kyautar kuɗi a bana, sama da Naira Miliyan 250 da ya raba a bara.

A baran ne dai Davido ya raba wa gidajen marayu Naira Miliyan 250 a fadin kasar nan bayan da ya sanar da a tallafa masa da kudi, inda kamar wasa, aka tara masa miliyan 150, shi kuma ya cika miliyan 100 su ka zama 250 sai ya raba wa marasa galihu a ƙasar.

Sai dai kuma a bana, yayin da ya ke tunkarar cika shekaru 30 da haihuwa, Davido ya yi alkawarin cewa a bikin zai raba kyautar kuɗi ta ban-mamaki ga ƴan Nijeriya.

Da ya wallafa a shafinsa na twitter, Davido ya ce “tallafin kuɗin bana zai ɗara na bara.”