Home Labarai Zan sadakar da tarar N800,000 da a ka yi wa Ganduje a kaina- Jaafar Jaafar

Zan sadakar da tarar N800,000 da a ka yi wa Ganduje a kaina- Jaafar Jaafar

0
Zan sadakar da tarar N800,000 da a ka yi wa Ganduje a kaina- Jaafar Jaafar

 

Mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya baiyana cewa zai yi amfani da tarar N800,000 ɗin da kotu ta yi wa gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Ganduje dai ya kai Jaafar babbar kotu da ke Kano ne a 2018 bisa laifin ɓace da ƙage bayan da fitaccen ɗan jaridan ya wallafa wasu faya-fayan bidiyo da su ka nuna gwamnan ya na amsar dalolin Amurka a matsayin na goro.

To amma daga bisani, sai kotun ta baiwa Ganduje umarni da ya biya Jaafar ɗin N800,000 domin ɓata masa lokaci bayan da gwamnan ya janye ƙarar.

A wata hira da Jaafar ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano, Jaafar ya baiyana cewa zai bayar da gaba ɗaya kuɗin ga shirin In da ran ka da ke ɗauke da wani ɓangare na neman taimakon lafiya da kuɗin makaranta a gidan rediyon.

Jaafar ya ƙara da cewa zai cika N200,000 a kan kuɗin su zama N1,000,000 domin a taimakawa masu ƙaramin ƙarfi.

A yanzu haka Jaafar ya samu mafaka a ƙasar Ingila bayan da ya yi ƙorafin cewa a na barazana ga rayuwarsa sakamakon fallasa faya-fayan bidiyon dalar da ya yi.