
Bulaliyar majalisar dattijai, Orji Uzo Kalu ya baiyana cewa sai ya fi kofin Super Eagles, Gernot Rohr ƙoƙari da a ce zai zama kocin tawogar ƙwallon ƙafar ƙasar.
Kalu ya faɗai hakan ne domin ya nuna ɓacin ransa a wasan da Super Eagles ɗin ta yi 1-1 da Cape Verde a wasan share fagen zuwa gasar kofin duniya ta 2022 a ranar Talata.
Duk da Super Eagles ɗin ta yi kunnen doki, ta samu rikicin buga wasan tantancewa na gasar.
Amma duk da haka Kalu bai ji dadin sakamakon ba inda ya faɗawa kamfanin dillancin labarai, NAN cewa wasan, da wanda ya yi kafin nan duk ba su yi kyau ba saboda Rohr bai yi amfani da ƙwarewa a wasannin ba, inda ya ce ya kamata a kore shi.
“Gaskiya Rohr ba ya ƙarawa ƴan wasansa ƙaimi Saboda ba shi da wata hikima ta koyarwa. Ko ni sai na bunƙasa ƙwazon ƴan wasa sama da shi.
“Gaskiya ba koci ba ne mai kyau. Ni bana ganin iyawarsa kwata-kwata. Ba shi da zafi, ba shi da hikima , ba shi da hikimar taka leda mai kyau shi ya sa Ni gaba ɗaya salon wasansa ba ya burge ni,” in ji Kalu.
Kalu ya ƙara da cewa zai so a samu koci na cikin gida in dai za a riƙa biyan shi yadda ya dace.