Home Siyasa 2023: Zan ziyarci dukka mazaɓu 484 na Kano na ji matsalolinsu don na magance su in na ci zaɓe — Salihu

2023: Zan ziyarci dukka mazaɓu 484 na Kano na ji matsalolinsu don na magance su in na ci zaɓe — Salihu

0
2023: Zan ziyarci dukka mazaɓu 484 na Kano na ji matsalolinsu don na magance su in na ci zaɓe — Salihu

 

 

Ɗan takarar Gwamna a jamiyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa, nan bada jimawa ba zai kai ziyara ɗaukacin mazaɓun Kano ɗari huɗu da tamanin da huɗu don duba halin da ƴan jam’iyyar da al’ummar yankin su ke ciki.

Yakasai ya kuma jaddada aniyarsa ta cigaba da kai ziyara Kananan Hukumomin jihar don sanin halin da yankunan su ke domin ya san ta yadda zai tunkari matsalolin idan ya zama gwamna.

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa ga manema labarai a yau Talata a Kano.

Ya kuma bayyana cewa sun zagaya wasu kananan hukumomin jihar nan don ganewa idonsu halin da al’ummar wadannan yankunan ke ciki, inda ya ci alwashin da zarar ya samu nasara a babban zaɓen 2023 zai yi iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen magance matsalolin dake addabar yankunan.

Ya kuma bayyana cewar wannan ziyara ta kunshi sada zumunci da neman tubarrakin manyan kowacce Karamar Hukumar, kamar malamai da hakimai da dagatai da masu unguwanni.

Yakasai ya ƙara da cewa sun kuma ziyararci da dama daga tsofaffin jagororin jamiyyar tun lokacin da take NEPU, inda su ka nemi shawara da kuma tabarraki da ga gare su.

Dan takarar Gwamnan ya kuma baiwa magoya bayansu dama sauran al’ummar jihar nan tabbacin idan P R P ta kafa gwamnati zasu sauko kasa don tafiya da kowa ta hanyar sauraron matsalolin al’umma tare da ganin ta tabbata magance musu shi.

Daganan sai yayi kira ga yan takarkarinsu da su cigaba da bashi hadin kai da goyon baya dari bisa dari, wajen ganin an cimma nasarar da ake da bukata, inda yace shi kansa zai iya tafiyar da al’amuran jamiyyar ba ba tare da goyon bayan su ba.