Home Labarai ZANGA-ZANGA: Ni ban yi fatan a yi juyin mulki ba — IBB

ZANGA-ZANGA: Ni ban yi fatan a yi juyin mulki ba — IBB

0
ZANGA-ZANGA: Ni ban yi fatan a yi juyin mulki ba — IBB

Tsohon shugaban ƙasa na soji, Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, ya nesanta kan sa dava wani sako da aka wallafa a shafin X, inda ake kira da sojoji su yi juyin mulki a Nijeriya.

A wata sanarwa da ofishin yada labaran IBB ya fitar, mai ɗauke da sahannun Alh. Mahmoud Abdullahi, IBB ya ce rahoton na karya ne.

Ya ce shafin na X, mai suna @General_Ibbro ya taba buga cewa IBB ya zabi wani dan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, kuma sakon na karya ne.

Hasali ma, a cewar Abdullahi, shafin na ƙarya ne, inda ya kara da cewa “ɓatagari ne su ka ƙirƙiro shi, har da saka hoton mai gida da tambarin Nijeriya kuma na karya ne, ba na mai gida ba ne,” in ji shi.