
Bayan kowa ya gama tofa albarkacin bakinsa, kuma anyi zanga-zanga an ga abun da ya faru, ga sharhi na.
1. Kowa a Nigeria, harda Tinubu ya yadda cewa mafi yawancin yan Nigeria suna cikin mawuyacin halin rayuwa musamman akan abinci da tsaro. Abun tambaya anan shine, shin za’a iya cigaba da tafiya a haka? Ko shakka babu mafi yawancin mutane 90% sun san ba zai yiwu a cigaba da rayuwa a haka ba. Wato dole ne sai an gyara domin a kawo wa talaka sauki, kuma dole ne wannan gyaran shugabanni yan siyasa sune zasu gyara.
2. Matsalar shine shin yan siyasa suna da imanin da zasu gyara da kansu ko sai anyi musu dole, a nan gizon yake saqa. Duk wani mai hankali ya san wannan mugayen yan siyasar tamu, makaryata, mayaudara, marasa Imani, azzalumai ba zasu taba gyarawa da kansu ba sai an tirsasa su.
3. Abu na gaba ta yaya zaa tirsasasu su gyara, a nan aka samu mafi girman sabani, talakawa sunce ayi bore, malamai sunce ayi addu’a tare da yiwa shugabanni nasiha da waazi, talakawa kuma suyi hakuri suyi ta kiran Allah domin samun mafita. Hakika komai yayi zafi maganinsa Allah, kuma rantsuwa ba kaffara malamai sunyi gaskiya, idan aka koma ga Allah tabbas Allah zai kawo mafita. Amma fa ku sani babu wanda yayi alkawari da Allah cewa ga lokacin da zai kawo mafitar, maana ana iya shafe shekara 100 ana azabtuwa kafin Allah ya kawo mafitarsa, wanda suka yi hakuri suka mutu suyi shahada su shiga Aljannah, wasu zasu galabaita har Allah yayi lamarinsa.
4. Misali sahabbai suna tare da Manzan Allah tsanani yayi tsanani suka ce masa “مَتَىٰ نَصْرُ ٱللَّهِ” yaushe nasarar ubangiji zata zo “suratul baqara aya 214”, duka da yake ayar ta cigaba da cewa ” أَلَآ إِنَّ نَصْرَ ٱللَّهِ قَرِيبٌۭ” lallai taimakon ubangiji yana kusa, kusan ubangiji ba lalle ne ta zama irin kusan dan-adam ba. Misali yau shekara 77 tun 1948 isaraila take azabtar da falestinawa kuma duk duniya ana musu addua Allah ya kawo musu mafita da galaba akan yahudawa, kuma tabbas ko shakka babu nasarar tana nan tafe amma har yanzu Allah cikin hikimarsa bai kaddara zuwan ta ba. Wanda suka mutu sunyi shahada, wasu zun galabaita yayin da ake jiran mafitar Ubangiji. Shin yan Nigeria suna da wannan imanin irin na sahabbai da palastinawa, da jumuri da juriya zasu iya irin wannan hakuri ko baza su iya ba.
5. Magana ta Gaskiya shine Yan Nigeria basu da wannan imanin, don haka ba zasu iya ba, toh menene abun yi ? Mafita yanzu shine a tursasa shugabanni su gyara, toh ta yaya zaa tursasa su ? Shin idan anyi musu waazi, da nasiha, da fadakarwa, da conference, da townhall, da symposium, da rubuce-rubuce zasu gyara ? Gaskiya itace wannan ba zai sa su gyara ba domin akasarinsu basu da Imani kamar yadda Sheikh Ibrahim Khalil ya fada, dole sai anyi gwagwarmaya zaa gyara. Toh amma fah malamai sunce bore ga shugabanni haramun ne, ya zaayi kenan. Kamar barawo ne ya shigo maka gida kace zaka yi masa waazi da nasiha, haka muke da shugabannin mu na siyasa, ko dai ka barshi yaci zarafinka, kokuma kayi kukan kura ka rungume shi, ko kaci nasara ko kayi shahada, haka abun yake.
6. Hadisin da malamai suke kafa hujja dashi manzon Allah S.A.W cewa yayi zaayi shugabanni da zasu muzguna muku, abin da za kuyi ku basu haqqinsu, malamai sunyi tawili akan cewa idan aka bijire musu to an sabawa maganar Annabi, amma fa ni a guntun ilimina Annabi cewa yayi a basu haqqinsu, haqqinsu kuwa shine abin da matsayinsu ya basu, shugabanci irin na demokradiyya haqqi ne akan shugaba na demokradiyya ayi masa zanga-zanga amma ta lumana. Don haka idan a demokradiyyance kayiwa shugaban demokradiyya zanga-zanga ta lumana toh fah ka bashi hakkinsa da matsayinsa ya bashi ne ba saba masa koh sabawa haqqinsa kayi ba.
7. A ina gizon yake saka, shin zamu iya yin zanga-zanga ta lumana ? Malamai har da mutane masu hankali da hangen nesa sunyi ittifaqin ba zaa iya yin zanga-zanga ta lumana ba, kuma gaskiya suke fada. Amma fa ku sani WALLAHI ko Alkur’ani malamai zasu ce alumma su dinga hadiyewa kuma su dinga yin kiyamul-laili kullun tare da shan rubutu kullun, wallahi alumma ba zasu iya zama da yunwa da rashin tsaro ba kamar yadda Allah SWT yace “ٱلَّذِىٓ أَطْعَمَهُم مِّن جُوعٍۢ وَءَامَنَهُم مِّنْ خَوْفٍۭ” Allah shine wanda ya bawa mutanen Quraishi niima ta abinci da ta tsaro don haka su gode masa “suratul Quraish aya 4”. Wato wannan shine matakin zaman lafiya guda biyu da suka zama dole a kowacce alumma. Toh ina mafita ?
8. A nan ina tare da Barr AUDU BULAMA BUKARTI Audu Bulama Bukarti, mafita shine da malaman addini, da sarakuna, da hakimai, da masu unguwanni, da manyan mutane, da yan kwadago, da yan kasuwa, da malaman jamia, da manyan maaikatan gwamnati, da kungiyoyi duk su hada kai su fito su jagoranci zanga-zanga ta lumana ko kuma zaman dueshan, kar su bar matasa yan zauna gari banza su dauki mataki da kansu. Ka kwatanta gidan Qadiriyya sun jagoranci zaman dueshan a cikin gari, Prof Sani rijiyar lemu da mutanensa sun jagoranci ta Nasarawa, malaman tijjaniyya sun jagoranci zaman wajen gari, malaman jamia sun jagoranci dalibai a zauna a maaikatun gwamnati. Ko shakka babu ba zaa samu bata gari suyi taaddanci ba, idan ma an samu abun zai matukar takaita sosai, kuma a cikin awa 24 gwamnati zata dauki matakin da zai kawo sauki nan take.
9. Hatsarin shine wallahi ko ayi wannan Shirin ko kuma idan aka cigaba a haka toh rantsuwa ba kaffara bayan wani dan lokaci wata 6 ko sama da haka wata zanga-zangar zata sake barkewa wadda tafi wannan muni, domin mayunwaci bashi da hankali “A hungry man is an angry man”. Idan kuma har baayi zanga-zanga ba to ko shakka babu gari sai ya gagari kowa fita da zama, domin duk wannan matasan sai sun koma barayi da yan fashi domin samar wa kansu mafita.
10. A karshe ni bana goyon bayan irin zanga-zangar da akayi yanzu, domin ba tada shugabanci, ba tada tsari, ba tada doka, ko martin luther king da yayi tawayen kwato wa bakake haqqinsu a amurka sai da ya saka dokoki guda hudu. Amma ko sau daya bana ganin laifin wanda sukayi zanga-zanga, nafi ganin laifin malamai, da sarakuna, manyan mutane domin sune suka ki bawa talakawa mafita. Haka zalika ina takaicin wadanda aka yiwa barna kuma sukayi asara, ina fatan Allah ya mayar musu da alkhairi, amma wannan kaida ce ta juyin juya hali dole ne sai anyi barna an zubar da jini anyi asara “collateral damage”, haka abun yake tun farkon duniya har gobe, kuma ni na karbi wannan a matsayin kaidar gwagwarmaya musamman a irin halin da muke ciki, sakamakon zalincin yan siyasa.
Allah ubangiji mun tuba ba dan halin mu ba, Allah ka dube mu da idon rahama, Allah ka kawo wa bayinka sauqi, Allah kayi mana maganin azzaluman shugabanni, Allah ka bawa alummar mu dama musulmi baki daya mafita da zaman lafiya.
Engr Muhammad Attahir (Suraj) dalibin ilimin addini da na boko, ya rubuto daga Bangkok, Thailand.