Home Labarai Zanga-zangar matsin rayuwa ta fara rage karsashi a Abuja

Zanga-zangar matsin rayuwa ta fara rage karsashi a Abuja

0
Zanga-zangar matsin rayuwa ta fara rage karsashi a Abuja

Yayin da aka shiga rana ta 3 ta zanga-zangar adawa da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, wacce aka tsara yi daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta , da alama ta fara rage karsashi a birnin tarayya Abuja.

A wani bangare na takaita zanga zangar mahukunta a birnin tarayya Abuja sun takaice ta a iya filin wasa na MKO Abiola.

Kodayake, a ranar farko masu zanga-zangar sun nufi filin taro na Eagles Square inda ƴan sanda suka tarwatsa su, sai su ka wuce filin wasa na MKO Abiola.

Daily Trust ta rawaito cewa a rana ta uku ta zanga-zangar babu ko mutum da ya fito, sai dai an hangi jami’an ƴan sanda da ƴan jarida a tsaye sai dai babu masu zanga-zangar.

Sannan wakilin Daily Trust ya jiyo wani jami’in ɗansanda na shaguɓe ga masu zanga-zangar cewa “sun tafi hutun karshen mako”.

Sai dai daga bisani wasu masu zanga-zanga da basu wuce su goma sha uku ba sun taho suna wake-wake na nuna adawa da halin da suka ce gwamnatin tarayya ta jefa yan kasa.

Duk wuraren da aka yi zanga-zangar a kwanaki biyu da suka shige yanzu babu kowa, inda hakan ke nuna cewa zanga-zangar ta rage karsashi.

Daily Trust