Home Wasanni An zargi Iran da amfani da Namiji a matsayin mace a kwallon mata

An zargi Iran da amfani da Namiji a matsayin mace a kwallon mata

0
An zargi Iran da amfani da Namiji a matsayin mace a kwallon mata

 

Kasar Jordan ta zargi kasar Iran da sanya Namiji a matsayin gola a gasar kwallon kafa ta mata da aka buga tsakaninsu. Golan wanda aka ce macece ce ya kade kwallo biyu a cikin hudun da aka buga masa.

Sai dai bayan tashi daga wasan kasar Jordan ta nuna rashin gamsuwa da wasan, inda ta bayyana cewar Golan Iran namiji ne, ba mace ba. Tuni dai suka aike da takardar koke zuwa ga hukumar kula da kwallon mata ta Asia Cup da ake bugawa yanzu haka.

Golan da aka bayyana sunansa da Zohreh Koudaei, shekararsa 32.

Kasar ta Jordan ta bukaci ayi masa binciken kwakwaf dan gano cewar mace ce ko namiji.