
Babbar Kotun jiha mai zamanta a Mila road ta bada belin Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge, Ibrahim Abdullahi Shehi.
A yau Laraba ne dai Hukumar yaƙi da Cin-hanci mai zaman kanta, ICPC ta gurfanar da Shehi kan laifuka huɗu da suka shafi almundahana a kan kuɗaɗen harajin da ƙaramar hukumar ke tarawa.
Laifukan sun haɗa da yin amfani da ikon mulki ya fifita wasu ma’aikata a kan wasu, baiwa wasu masu karɓar haraji kaso 20 na kuɗin da a ka tara har karo huɗu da kuma sauran laifuka sa su ka shafi almundahana.
Bayan an karanta masa laifukansa, sai Shehi ya musa.
Daga bisani alƙalin kotun, Jamilu Sulaiman ya bada belin shugaban ƙaramar hukumar amma sai ya bada Naira dubu ɗari biyar.
Alƙalin ya ce ya bada belin Shehin ne sabo da shi mai mulki ne.
Ya ɗage zaman sai ranar 17 ga Janairu, 2022 domin sauraron ƙara.
Daily Nigerian Hausa