
Babbar Kotu a Jihar Kano da ke titin Miller ta sanya ranar 7 ga watan Maris domin sauraron ƙarar da a ka shigar a kan Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge, Mohammed Abdullahi Shehi kan zargin almundahanar kuɗaɗe.
A tuna cewa a ƙarshen 2021 ne Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta ICPC ta maka Shehi a kotu a bisa zargin yin sama-da-faɗi da kuɗaɗen haraji da ƙaramar hukumar ta ke karɓa.
Hukumar na tuhumar Shehi da laifukan huɗu na zargin yin kwana da kuɗaɗen haraji da a ke karɓa a karamar hukumar.
Da a ka dawo zaman a yau, alƙalin kotun, Jamilu Shehu Suleiman, ya bada belin Shugaban Ƙaramar Hukumar.
Alƙalin ya ce belin ba zai cika ba sai Shehi ya biya naira dubu 500.
Alƙali Suleiman ya dage sauraron ƙarar zuwa 7 ga watan Maris.