Home Labarai Zargin ɓatanci: Deborah ta tsallaka layin da ba a tsallaka wa, in ji Maqari

Zargin ɓatanci: Deborah ta tsallaka layin da ba a tsallaka wa, in ji Maqari

0
Zargin ɓatanci: Deborah ta tsallaka layin da ba a tsallaka wa, in ji Maqari

 

Limamin babban masallacin kasa na Abuja, Ibrahim Maqari, ya mayar da martani a kan kisan da aka yi wa Deborah Yakubu, wata daliba Kirista a jihar Sakkwato, bisa zarginta da ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW), inda ya ce marigayiyar ta tsallaka layin da ba a tsallaka wa.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu ɗaliban kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto suka kashe wata ɗaliba bisa zargin ɓatanci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar sakon murya da ts aike ta kafar WhatsApp.
Tuni dai gwamnatin jihar ta rufe makarantar, yayin da ƴan sanda suka cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin.
Da yake mayar da martani game da abin da ya faru ta sahihin shafin sa na Twitter,  Maqari ya jaddada cewa Musulmai na da wasu jajayen layukan da ba a tsallaka su.
“Ya kamata kowa ya sani cewa mu Musulmai mu na da wasu jajayen layika da dole ma ba za a tsallaka su ba
“Darajar Annabi SAW ita ce kan gaba a jajayen layukan nan. Idan har ba a magance koke-kokenmu yadda ya kamata ba, to bai kamata a rika sukar mu idan mu ka magance da kan mu ba,” inji shi.