
A jiya Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja, ta ce dakataccen Akanta Janar, AGF, Ahmed Idris da wasu mutane uku, sun kai kansu hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC domin neman sasantawa, dangane da batun da ke gaban shari’ar su bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109.
Idris, Mataimakinsa na musamman, Godfrey Olusegun Akindele; da wani darakta a ofishin AGF, Mohammed Kudu Usman da wani kamfani mai alaka da Idris – Kasuwar Kayayyaki da ta Gezawa – an gurfanar da su ne a ranar 22 ga watan Yuli a kan tuhume-tuhume 14 da suka hada da hada-hadar kudi, sata da kuma karya amana.
Jaridar The Nation ta rswaito cewa, Babban Lauyan da ke shigar da kara, Rotimi Jacobs (SAN) ya ce Idris ya tuntube shi ta hannun wani bangare na uku domin gudanar da wani taro kan hanyoyin da za a bi domin cimma matsaya na sasantawa a matsayin mafita.
Jacobs ya kara da cewa tun da sashe na 270 na hukumar kula da shari’ar laifuka (ACJA) ya bayar da damar yin sulhu, ya amince ya gana da wadanda ake kara a ofishin EFCC, amma da sharadin cewa lauyoyinsu da masu binciken EFCC (wadanda suka gudanar da shari’ar) dole ne su halarta.
Ya ce taron da aka shirya yi a ranar da ta gabata (Talata) bai yi nasara ba saboda wadanda ake kara sun zo ba tare da lauyoyinsu ba.
Jacobs ya kara da cewa lauyan wanda ake kara na farko (Idris), wanda ya bayyana sunansa da Kanayo, ya zo inda za su gana da korafin cewa ba a dauke su (lauyoyin wadanda ake kara).
“Wanda ake tuhuma na farko ya aiko mani da wani mutum na uku cewa yana son ganawar sulhu kuma yana so ya sadu da ni. Wato (Talata) da safe. Kuma na amsa da cewa ba zan iya saduwa da wadanda ake tuhuma ba idan babu lauyan su.