
Lauyan nan mai fafutukar ƴancin ɗan adam, Femi Falana, ya shaidawa Babbar Kotun Tarayya a Kano cewa rigar kariyar da ke jikin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta tuɓe tun a ranar 29 ga watan Mayu.
A tuna cewa a ranar 7 ga watan Yuli ne dai kotu ta hana hukumar karbar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano, PCACC, kama Ganduje, iyalansa ko abokan siyasar sa har sai an saurari ƙorafin da ya shigar a kotu.
Sai dai kuma Lauyan na PCACC ya ce kariyar ta Ganduje ta kare tun ranar 29 ga Mayu.
Falana ya ce shari’ar ta shafi al’umma ba wai ta Ganduje ba ce a kan kansa, inda ya kara da cewa kotun ba ta da hurumin da za ta kare shi.
A karshe Falana ya bukaci kotun ta kori wannan umarnin na dakatar da kamo Ganduje.
Alkalin kotun, A. M. Liman ya dage zaman sai ran 22 ga Satumba domin yanke hukunci.