
A yau Alhamis ne babban lauyan jihar Kano kuma kwamishinan shari’a, Musa Abdullahi Lawan, ya wanke shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga zargin kisan kai.
Lawan, wanda ya ke zantawa da manema labarai a Kano, ya ce bisa la’akari da bayanan da aka yi a baya, ma’aikatar ba za ta iya tabbatar da tuhume-tuhumen laifuffukan da suka hada da hada baki, tada zaune tsaye, saka wita da kuma kisan gilla ga Doguwa ba.
“Ba mu iya samun isassun shaidun da za su danganta Doguwa da laifukan da aka ambata ba, la’akari da kwararan hujjojin da aka bayar a kan sa,” in ji Kwamishinan.
Ya ce iƙirarin waɗanda su ka ce laifin Doguwa ne cike ya ke da cin karo da juna kuma ba su iya samun shaidar likita da ke tabbatar da mutuwar wadanda aka mutun ba.
“Doka a bayyane ta ke cewa ba za a iya tabbatar da zargin da Doguwa ya yi na kashe mutane ba.
“Mun dogara ne a kan bayanan binciken da ‘yan sanda suka yi kamar yadda yake kunshe a cikin kundin bayanan lamarin da aka aiko daga FCID ba tare da jin tsoro, alfarma ko son zuciya ba,” in ji shi.