Home Labarai A na zargin Mai-unguwa da sayar da ruwan rijiyar al’umma a Kano

A na zargin Mai-unguwa da sayar da ruwan rijiyar al’umma a Kano

0
A na zargin Mai-unguwa da sayar da ruwan rijiyar al’umma a Kano
A na zargin Mai-unguwar Kuwet da ke yankin Rimin Kebe, Ƙaramar Hukumar Ungoggo a jihar Kano.
Tun da fari dai wata gidauniya ce, mai suna Widi Jalo Foundation ta gina rijiyar ta burtsatse a unguwar bisa roƙon al’ummar yankin.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa bayan an gina rijiyar ne, sai a ka gano Mai-unguwar yankin, Alhaji Nuhu Muhammad na sayar da ruwan, maimakon al’umma su amfana a kyauta kamar yadda gidauniyar ta tanada.
Wakilin gidauniyar, Yahaya Sufi Abbas, ya ce sun samu ƙorafin cewa Mai-unguwar na sayar da ruwan, inda su ka yi maza su ka same shi domin ya daina.
A cewar Abbas, ko da a gina rijiyar, bisa shawarar dagacin yankin, an ya je cewa a riƙa sayar da kan famfo ɗaya domin a samu kuɗin da za a riƙa gyaran rijiyar idan ta lalace.
Ya ƙara da cewa shi kuma Mai-unguwar kawai sai ya ke sayar da suka kan famfunan, kuma an masa magana ya ce wai ba zai daina ba sai dai a kai shi duk inda za a kai shi.
“Mu dai mun faɗa masa cewa za mu danƙa rijiyar ga hannun hukuma kawai tunda dai mu fisabilillahi mu ka gina rijiyar nan domin alfanon mutanen unguwar kamar yadda su ka nema daga gare mu,” in ji Abbas.
Da a ka tuntuɓi Mai-unguwar, ya ce ya yanke shawarar sayar da ruwan ne domin a samu kuɗin gyaran rijiyar idan ta lalace.
Ya kuma ce tunda haka ta faru, to zai kulle rijiyar gaba ɗaya kuma zai gina wata da kansa, inda ya ƙara da cewa dama ba wai don bukatar kansa ya ke sayar da ruwan ba sai dan a samu na gyaran rijiyar idan ta lalace.
Sai dai kuma al’ummar yankin na kira ga hukumomi da su kawo musu ɗauki don ganin an yi maslaha don su ci gaba da amfanar rijiyar