Home Labarai Zargin safarar sassan jiki: Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki lauyoyi domin kare Ekweremadu da matarsa

Zargin safarar sassan jiki: Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki lauyoyi domin kare Ekweremadu da matarsa

0
Zargin safarar sassan jiki: Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki lauyoyi domin kare Ekweremadu da matarsa

 

 

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana cewa ofishin jakadancin Nijeriya na Birtaniya ya ɗauki lauyoyi da za su kare Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, waɗanda a halin yanzu ake tsare da su kan zargin da ake yi na safarar sassan jiki.

Lawan ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yayin da ya ke bayar da cikakken bayanin ganawar sirri da majalisar ta yi kafin fara zaman majalisar.

A cewar Lawan, wata tawaga daga kwamitinta mai kula da harkokin ƙasashen waje za ta tashi daga Nijeriya zuwa Landan ranar 1 ga watan Yuli, 2022, domin kai ziyara ga Sanatan da ke cikin rikici.

Lawan ya ƙara da cewa matakin da aka ɗauka na shiga maganar ta kama Ekweremadu da tsare shi ya zo ne sakamakon rahoton da babban jakadan Nijeriya a Landan ya samu.

Ya kuma bayyana cewa majalisar dattawa za ta tuntuɓi ma’aikatar harkokin wajen kasar da kuma ofishin jakadancin Nijeriya a birnin Landan kan kama sanata Ike Ekweremadu da ‘yan sandan birnin Landan suka yi kwanan nan a ƙasar Birtaniya.

Ya ce: “Na yi ganawar sirri da babban kwamishinanmu na Najeriya a kasar Birtaniya, Alhaji Isola Sarafa, wanda ya yi matukar kokari wajen kulla alaka da abokin aikinmu, wanda ya samu nasarar shigar da tawagarsa a kotu da ke Uxbridge inda Ekweremadu”