
Ana zargin ƴan kungiyar sintiri (vigilante) da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Dabai, da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
Shi dai Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Ƙur’ani ne a unguwar, inda yake da ɗaruruwan almajirai.
Ana zargin ƴan kungiyar sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunkurin satar yaro.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa dan malamin, Ibrahim ya sheda mata cewa, ”Mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa a wata bola.
Sai ya je ya dauki yaron, sai kawai wata mata da ta hango shi, sai ta kwarma ihu tana ce masa ɓarawon jariri.”
”Kururuwar da matar ta yi ce ta janyo ‘yan kungiyar sintirin da sauran jama’ar unguwar wadanda suka rufe shi da duka,” in ji dan.
Ya ƙara da cewa, ”daga nan sai suka tafi da shi ofishinsu suka ci gaba da dukansa. Daga baya ya fadi a sume.”
Ya ce,” Bayan da wasu ‘yan unguwar suka gane shi sai suka garzaya da shi asibiti, inda ya cika a hanya.”
Ɗan malamin ya sheda wa jaridar cewa ‘yan-sanda sun kama shugaban ‘yan-sintirin na unguwar, mai suna Munkaila, inda ake bincikensa a caji ofis na Rijiyar Zaki.
Ita ma rundunar ƴan sanda a jihar Kano, ta bakin kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama mutane 6 da a ke zargin na da hannu a kisan, kamar yadda ya shaida wa Freedom Radio.