
Yayin da a ke zaton NNPP zai koma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Peter Obi, ya koma jam’iyyar Labour Party, LP, domin tabbatar da aniyarsa ta shugabancin ƙasa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a ranar Talata ne Obi ya fice daga jam’iyyar PDP, yana mai alakanta matakin da ya dauka kan “alamuran da ke faruwa a jam’iyyar a kwanakin baya.
Jim kaɗan bayan ficewar ta sa daga PDP, sai a ka ga hotunansa da jagoran jam’iyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso na yawo a kafafen sadarwa, inda a ke riƙa raɗe-raɗin cewa jam’iyar zai koma, har a bashi mataimakin ɗan takarar shugaban kasa.
Sai dai kuma da yake bayyana yadda ya shiga sabuwar jam’iyyar siyasa ta shafinsa na Twitter, Obi ya ce “tsarin cimma burinmu yana da muhimmanci kuma tushe ne na ci gaba”.
Ya ce: “Ina godiya ga daukacin ‘yan Nijeriya, musamman ma matasanmu da suka bi ni wajen ganin an dawo da kimar Nijeriya gaba daya. Wannan aikin naku ne kuma na makomar yaranku. Ni dai ɗan jagora ne.
“Tun da na fice daga PDP saboda al’amuran da suka ci karo da mutumtaks da ka’idata, na tuntubi bangarori daban-daban da na jama’a don ganin ba mu samu tasgaro a hanyar zuwa inda muke so ba.
“A gare ni, tsarin cimma burinmu yana da mahimmanci kamar abin da mutum zai yi bayan haka.