
Zazzaɓin Lassa ya kashe mutane takwas a Jihar Gombe daga watan Febrairuzuwa yanzu, in ji Dakta Nuhu Bile, ƙwararren a fannin cututtuka masu yaɗuwa na Ma’aikatar Lafiya ta jihar.
Bile, a wata ganawa a jiya Laraba da Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN a Gombe ya ce kawo yanzu, mutane 225 a ka yi wa gwajin cutar a jihar.
A cewar sa, 20 daga cikin waɗanda a ka yi wa gwajin su na ɗauke da cutar, inda 10 kuma an musu magani an sallame su.
Ya ƙara da cewa mutum biyu da a ka tabbatar sun kamu da cutar su na can a kwance a na duba su, inda takwas kuma su ke jiran ko-ta-kwana.
Bile ya bayyana cewa an samu bullar cutar ne a ƙananan hukumomin Balanga, Funakaye, Kwami, Kaltungo, Nafada da Gombe.
Sai dai kuma ya ce garin Dogonruwa da ke Ƙaramar Hukumar Kaltungo ne su ka fi yawan masu ɗauke da cutar a jihar.
Ya ce bayan da a ka samu bullar cutar a jikin mutum 5 a watan Fabrairu, tuni gwamnatin jihar ta tashi tsaye don daƙile yaɗuwar ta a jihar.