Home Wasanni Zidane ya bukaci hukumomi a Real Madrid da su gaggauta dauko masa Salah

Zidane ya bukaci hukumomi a Real Madrid da su gaggauta dauko masa Salah

0
Zidane ya bukaci hukumomi a Real Madrid da su gaggauta dauko masa Salah

Daga Hassan Y.A. Malik

Kocin Real Madrid, Zinadine Zidane ya yi kira ga shugaban majalisar gudanarwar kungiyar, Florentino Perez da ya dauko masa dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah a karshen kakar wasanni ta bana.

Zidane ya bayyana cewa zuwan Salah zai kara karfin masu kai farmakin tawagar ta Real Madrid.

Zidane ya ci gaba da cewa ya fi bukatar Salah a Real Madrid sama da yadda ya ke bukatar Harry Kane, wanda shi ma ke cikin jerin ‘yan wasan da Madrid ke nema.

Sai dai kuma dole Real Madrid ta hakura har sai bayan gasar cin kofin duniya da za a buga a bana kafin ta nemi daukar Salah daga Liverpool.

Tauraron dan wasa Salah na haskawa a bana, inda dan wasan ya jefa kwallaye 32 a wasanni 38 da ya wakilci Liverpool